A yayin wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Mr. Mahama, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da noman cocoan a hukumance, yana mai sukar hukumar COCOBOD wadda ke kayyade farashin kayan gonar da cewa jami'anta na gogayya da manoma wajen neman riba.
Sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disambar ne dai ya bai wa John Dramani Mahama gagarumin rinjaye bayan korafin tsadar rayuwa da komabaya da 'yan kasar suka ce suna fuskanta a wajen noman cocoa da hakar ma'adanai.A ranar 7 ga watan Janairu mai kamawa ne dai ake sa ran za a rantsar da tsohon shugaban kasar ta Ghana a karo na biyu, kuma babban aikin da ke gabansa shi ne bunkasa tattalin arzikin jama'ar kasar da ya ragargaje a hannun gwamnatin jam'iyya mai mulkin kasar.