Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sanar da cewa, birnin Paris zai karbi bakuncin taron kasa da kasa a makonni masu zuwa don tara kudaden sake gina Lebanon, bayan da yakin da aka yi tsakanin mayakan Hezbollah da Isra'ila ya daidaita kasar. A yayin wata ziyara da yake gudanar a birnin Beirut, Macron ya bayyana goyon bayansa ga hukumomin Lebanon sakamakon warware dadadden rikicin siyasa da ya kai su ga zaben Michel Aoun a matsayin sabon shugaban kasa.
Karin bayani: Fara komawar 'yan gudun hijirar Lebanon
Sai dai wanda zai zama firaministan kasar Lebanon Nawaf Salam na fuskantar gagarumin kalubale na kafa gwamnati da za ta sa ido kan aikin sabunta gine-ginen da suka lalace, amma bayan tsagaita bude wuta na dindindi tsakanin Isra'ila da Hezbollah. Tuni ma dai shugaban kasar Faransa da ta yi wa Lebanon mulkin mallaka, ya yi kira ga kasashen duniya da su shirya don bayar da gagarumin taimako wajen samar da ababen more rayuwa a kasar.