Macron ya nemi goyon bayan Trump ga Ukraine

A yayin ganawar shugannin biyu a cikin ofishin shugaban Amurka na Oval Office da ke fadar White House, shugabannin sun jaddada rawar da kasashen Turai da kuma Volodymyr Zelensky na Ukraine za su taka wajen kawo karshen yakin.

Karin bayani: Kasashen EU na taron cika shekaru uku da fara yakin Ukraine 

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X gabanin ganawarsa da Trump, shugaba Macron ya ce Ukraine ta shafe shekara uku tana fama da kalubalen kare kan ta daga hare-haren Rasha, inda ya ce tabbas Ukraine ta taka rawar gani da kuma bajinta a yakin da ta ke gwabzawa da Rasha. Macron da ke ziyara Amurka a madadin shugabannnin kasashen Turai na kokarin shawo kan Trump kan bukatar goyon baya ga kasar Ukraine.

Karin bayani: Kasashen Turai za su tattauna makomar Ukraine

A baya-bayannan dai an samu rashin jituwa tsakanin Trump da Zelensky wanda hakan ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin Washington da Kiev.

 


News Source:   DW (dw.com)