Macron ya gana da Scholz kan Ukraine

Macron ya gana da Scholz kan Ukraine
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, don ganawa da shugaban gwamnati Olaf Sholz kan batutuwan da suka shafi makomar Ukraine bayan mamayar da Rasha ta yi mata.

Baya ga batun mamayar Rasha a Ukraine, batutuwan da za su dauki hankalin ganawar shugabannin biyu sun hada da halin da ake ciki a yankin Sahel na Afirka da alakar kasashe da yankin Balkan da manufofin EU a kan Chaina. Wannan dai shi ne karon farko da shugaban Faransan Emmanuel Macron ke ziyara  a Jamus, tun bayan zabensa karo na biyu a mastayin shugaban kasa a wa'adi na biyu na tsawon shekaru biyar. Ziyarar dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Rasha ke cika shekaru 77 da samun galaba a kan 'yan Nazi a Jamus yayin yakin duniya na biyu.


News Source:   DW (dw.com)