Ba a dai tantance musabbabin rugujewar ginin na Lagoas ba, ammai masu aikin ceto sun yi nasarar zakulo mutane 23 da suka samu munanan raunuka daga baraguzan ginin.
Rushewar gine-gine na neman zama ruwan dare a Najeriya sakamakon tauye ka'idojin gine-gine. Ko a watan Nuwamba, sai dai rushewar wani katafaren gini da ake kan ginawa a Legas ta yi sanadiyar mutuwar mutane 45 ciki har da ma'aikatan da suke aiki a wurin. Sannan mutane uku sun gamu da ajalinsu lokacin da wani coci a rushe a watan Janairu a Fatakwal da ke yankin Neja Delta
Bincike da wani masani dan kasar Afrika ta Kudu ya gudanar ya gano gine-gine 152 da suka ruguje a Legas tun daga shekarar 2005 wato a cikin shekaru 17.