Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa komai ya tsaya cak a filin jiragen saman Kenyatta da ke birnin Nairobi, inda ake dakon sanarwar da hukumomin kasar za su fitar kan wannan takaddama. Tuni dai gamayyar kungiyoyin ma'aikatan filin jiragen na Jomo Kenyatta suka fitar da sanarwar tafiya yajin aiki a shafinsu na X.
Karin bayani: Gobara a filin saukan jiragen saman Kenya
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda daruruwan matafiya da jakakkunansu ke tsaye carko-carko a filin jiragen na Nairobi, yayin da wasu ke kauracewa filin jirgin domin gudun abin da ka je ya zo.
Karin bayani: Kenya: Cin hanci ya addabi tashoshin jiragen ruwa
Matakin yajin aikin ya biyo bayan yarjejeniyar da hukumomin Kenyan suka rattaba hannu da wani kamfanin Indiya na Adani Group, wanda ya zuba hannun jarin Dalar Amurka biliyan $1.85 domin ci gaba da gudanar da filin jiragen saman na tsawon shekaru 30, matakin da ya haifar da cece-kuce a kasar ta Kenya.