'Yan tawayen M23 sun kwace iko da filin jirgin saman birnin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar Talata.
Wannan kamen ka iya katse babbar hanyar da agaji ke kaiwa ga dubban daruruwan mutane da suka rasa matsugunnansu.
A ranar Litinin ne M23 ta kwace iko da birnin Goma bayan wani gumurzu da dakarun DRC lamarin da ya lakume rayukan fararen hula.
Goma: An cinna wa ofishin jakadancin Faransa wuta a DRC
Masu zanga-zanga a babban birnin DRC Kinshasa sun cinna wuta kan ofishin jakadancin Faransa inda suke zargin akwai hannun kasar cikin abinda ke faruwa.
Wannan hali da birnin Goma ya shiga shi ne mafi muni tun a 2012, kuma rikicin ya faro ne shekara talatin da suka gabata tun bayan yakin kare dangin Rwanda.
Mutane na ficewa daga garin Goma
Har ila yau, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya tattauna da shugabannin kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da kuma Rwanda.
Mai magana da yawun MDD ne ya bada tabbacin tattaunawar wacce ya ce Guterres ya yi ta ne da ko wannensu daban-daban.
Mista Guterres ya kirasu ne kan yadda za a nemo bakin zaren warware yakin da 'yan tawayen M23 ke yi a birnin Goma na DRC.
Ko da a ranar Lahadi ma sai da kwamitin sulhu na MDD ya yi zama da jagorin kasashen biyu domin kawo karshen yakin da ya lakume rayukan al'umma.