Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce a yanzu lokaci ya yi da za a tsara makomar Gaza bayan shafe watanni 15 Isra'ila na gwabza yaki da Hamas a zirin.
Mista Scholz ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai a birnin Berlin albarkacin ziyarar Firaministan Denmark Mette Frederiksen.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai gana da shugaban Amurka Joe Biden kan Ukraine da Gaza
Ya kara da cewa ya kamata a samar da cigaba da za ta gyara siyasa da tattalin arzikin zirin Gaza biyo bayan sakin fursunonin yaki da ke hannun Hamas.
Shugaban na gwamnatin Jamus ya kuma ce ya na da matukar muhimmanci a ci gaba da bin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma sau da kafa tare da sako sauran Isra'ilawa dake hannun Hamas.
Scholz na Jamus ya jaddada aniyar aiki da Trump na Amurka
Har ila yau, Scholz ya fada cewa akwai bukatar kai wa Falasdinawa kayan agaji da magunguna kamar yadda ya kamata domin su farfado.