Libiya: Masu zanga-zanga sun kutsa majalisa

Libiya: Masu zanga-zanga sun kutsa majalisa
Masu zanga-zanga a Libiya sun kai farmaki kan ginin majalisar dokokin kasar da ke gabashin birnin Tobruk, don nuna fushin su kan tsadar rayuwa da rashin tabbas na makomar siyasar kasar.

Tashoshin talabijin da dama na kasar sun ruwaito yadda masu boren suka yi nasarar kutsawa cikin ginin majalisar dokokin Libiya tare da lalata abuwa da dama, inda ma wasu ke cewa an banka wuta a wani bangaren majalisar bayan ganin wasu hotunan bidiyon tirnikewar hayaki daga kewayen ginin.

Majalisar dokokin Libiya ta kasance a Tobruk, tun bayan barkewar rikicin gabashi da yammacin kasar a shekara ta 2014 bayan boren da ya kifar da gwamnatin tsohon Shugaba marigayi Moamer Kadhafi.

Firaministan rikon kwarya na gwamnatin Tripoli Abdulhamid Dbeibah, ya fada a shafinsa na Twitter cewa zai kara da murya ga masu zanga-zangar tare da yin kira da a gudanar da zabe.


News Source:   DW (dw.com)