Lebanon ta bukaci Isra'ila ta janye daga kudancin kasar

Sabon shugaban kasar Lebanon, Joseph Aoun ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta janye daga kudancin kasar nan da ranar 26 ga watan Janairun 2025 domin cike sharuddan tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra'ilar da kungiyar Hezbolla a 2024. A sakon da fadar shugaban kasar Lebanon ta wallafa a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, ta ce a wata ganawa a Beirut, Shugaba Aoun ya jadadda wa sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres cewa, ci gaba da kasancewar Isra'ila a wurin ya sabawa 'yancin Lebanon da ma yarjejeniyar da aka cimma wa.

Yarjejeniyar tsagaita bude wutar da ta fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwambar 2024 bayan da kasashen Amirka da Faransa suka shiga tsakani, ta bukaci sojojin Isra'ila da su janye daga yankin cikin kwanaki 60 kana Hezbolla ta kawar da dukannin mayakanta da kuma makamanta daga kudancin kasar.

Karin bayani: An samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon

Guterres ya ce, Majalisar Dinkin Duniya za ta yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin Isra'ila ta janye kafin wa'adin da aka dibar mata ya cika karkashin yarjejeniyar.

 


News Source:   DW (dw.com)