Lebanon: Kaucewa rikici a Gabas ta Tsakiya Kwamitin yana mai kira da a sassauta rikici bayan barkewar tashin hankali tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbullah. A cikin wani kuduri da aka amince da shi gaba daya, MDD ta yanke shawarar kara wa'adin rundunar har zuwa 31 ga Agusta, na shekara ta 2025. Rundunar ta UNIFIL mai kunshe da dakaru sama da dubu goma da ke aiki a kudancin Lebanon tun a shekara ta 1978 domin shiga tsakanin Hizbollah da Isra'ila. An karfafata tun bayan rikicin kwanaki 33 tsakanin Hezbollah da Isra'ila a lokacin bazara na shekara ta 2006.