Kyandar biri: AU ta ce adadin annobar na karuwa a Afrika

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa ta Afrika ta ce an samu bullar cutar a kasahen nahiyar 12, wanda yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 541, da adadin mace-macen ya kai kashi 2.89 bisa 100. Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar kyandar biri wato mpox a matsayin gagarumar annoba da ke bukatar daukin gaggawa.

Karin bayani: Kyandar biri na barazana a Afirka

Cutar dai ta fi kamari a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da annobar ta bazu a dukkan lardunan kasar 26. Rahotanni daga Burundi na cewa an samu rahotannin bullar cutar a mutane 173 da ake ci gaba da gudanar da bincike.

An dai samu rahotannin bullar cutar a karon farko a wajen nahiyar Afrika a kasashen Sweden da Pakistan.

 


News Source:   DW (dw.com)