Cutar kyanda ta kashe akalla kananan yara 157 a kasar Zimbabuwe da yankin Kudanin Afirka. Ministar yada labaran kasar Monica Mutsvangwa wacce ta sanar da haka a ranar Talata ta ce kawo yanzu an samu yara sama da 2,000 da cutar ta kama.
A farkon watan ne dai hukumomi suka sanar da barkewar cutar a kasar, kuma tun daga lokacin cutar da ke saurin kisan kananan yara ke kara yaduwa.
A watan Afrilun da ya gabata Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce cututtukan da a kan iya samun kariya daga gare su na kara yaduwa a Afirka, inda ta nuna damuwa kan yadda cutar ta kyanda ke saurin yaduwa a nahiyar.