Kwango ta zargi MDD da sakaci wajen daukar mataki kan M23

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya shaida wasikar bukatar dauki da jakadan Kwango a Majalisar Dinkin Duniya Zenon Mukongo ya gabatarwa zauren kwamitin sulhu na majalisar, biyo bayan hare-haren da 'yan tawayen M23 suka kaddamar a lardin Kivu da ke gabashin kasar.

Karin bayani: MDD ta yi gargadi kan rikicin Kwango

Jakadan ya ce gwamnatinsu ta samu rauni sakamakon rashin bada kulawar gaggawa daga majalisar, tun lokacin da 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda suka kwace iko da  babban birnin Goma na Arewacin Kivu da kuma Bukavu na lardin Kudancin Kivu.

 

 


News Source:   DW (dw.com)