Kwango na nazari kan dakarun MONUSCO

Kwango na nazari kan dakarun MONUSCO
Gwamnatin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango ta ce zata sake nazari kan shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga kasarta.

Hakan dai na zuwa ne biyo bayan mummunar zanga-zangar da 'yan kasar suka gudanar don nuna adawa da kasancewarsu sojojin a kasar.

Alkaluma na nuni da cewa kimanin fararen hula 29 da wasu dakarun MONUSCO hudu ne suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma a fadin kudancin kasar.

Masu boren dai na mika bukata ga dakarun wanzar da zaman lafiyar kan su fice daga Kwangon saboda gazawar da suka yi wajen kare su daga hare-haren kungiyoyin da ke tada kayar baya da suka shafe tsawon gomman shekaru suna cin karensu babu babbaka.

Rundunar ta MONUSCO ta jibge dakaru fiye da dubu 12 da kuma jami'an 'yan sanda 1600, sai dai zarge-zargen cin zarafin jama'a ya dabaibaye rundunar. 

Rikici tsakanin dakarun gwamnati da kuma kungiyar 'yan tawaye na M23 a gabashin kwango a baya-bayan nan ne ya rura wutar boren adawa da kasancewar dakarun MONUSCO a kasar.


News Source:   DW (dw.com)