Cibiyar dakile cututtuka masu saurin yaduwa ta Afrika ta ce ana sa ran shigiwar rigakafin sama da dubu 99,000, domin tunkarar rigakafin cutar ta kyandar biri gadan-gadan. Tuni dai dai jirgin ya bar birnin Copenhagen na kasar Denmark domin isa Jamhuriyar Kwango.
Karin bayani: Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika
A wani taron manema labarai da ya gudanar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da isar rigakafin na kamfanin Bavarian Nordic a matsayin gudummuwa daga kungiyar EU.
.