Wannan dai shi ne karon farko da shugaban 'yan tawayen M23, Corneille Nangaa ya bayyana kansa ga bainar jama'a a gabashin Kwango, tun bayan da dakarunsa suka kwace iko da birnin Bukavu makwani biyu da suka gabata. Sai dai kawo yanzu ba a san su waye suka tarwatsa taron ba, ko samun rahoton wadanda suke mutu ko suka jikkata a lokacin da lamarin ya faru.
Karin bayani: Mayakan M23 na kara kutsa kai yankunan gabashin Kwango
Kungiyar M23 na kokarin nuna wa jama'a cewa za ta dawo da doka da oda a birnin da ta kwace iko da shi, kana za ta sake bude tashoshin sifiri da kuma makaratu. Gwamnatin Kwango da Majalisar Dinkin Duniya da ma kasashen yammacin Turai na zargin Ruwanda da ke makwaftaka da Kwangon, da marawa 'yan tawayen M23 baya, zargin da Ruwandan ta dade ta musantawa.