Kwamittin yakin neman zaben Tump ya zargi Iran da yi masa kutse

Shafin siyasar Amirka ya bayyana cewa ya samu wasu sakwanni email dauke da bayanai daga offishin yakin neman zaben Donald Trump, daga wadanda ba a san ko su waye ba.

Lamarin da ya sanya kwamittin ya zargi Iran da hannu a cikin yi masa kutsen. Ko da yake bai gabatar da kwakwarar shaidar domin tabbatar da zargin nasa, sai dai ba da hujja da wani rahoto da masu bincike na Microsoft suka gabatar a wannan makon da ke nuna cewa, Iran na kokarin yin kutse cikin shafin kwamittin wani dan takarar shugaban kasar Amirka.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun kwamittin yakin neman zaben ya fitar, Steven Cheung ya ce Iran ta san cewa, Mista Trump ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen dagatar da salon mulkin Iran kamar yadda ya yi a cikin shekaru hudunsa na baya a fadar White House.

 


News Source:   DW (dw.com)