Tun da fari dai ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi ne ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da taro kan harin. A cikin wasikar da ya aika wa kwammitin sulhun, Araqchi ya ce ayyukan Isra'ila na zama babbar barazana ga zaman lafiya da kuma tsaron yankin da dama ke cikin halin tsaka mai wuya.
Karin bayani: Isra'ila ta ce ta kammala harin ramuwar gayya kan Iran
Rundunar sojin Isra'ila ta ce hare-haren da ta kai sun lalata wasu cibiyoyin yakin Iran da ke kusa da Tehran. Wannan dai na zaba ramuwar gayya ne ga hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai wa Isra'ila a ranar daya ga watan Octoban shekarar 2024.
Tuni dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukannin bangarorin da su mayar da wukakensu cikin kube, ciki har da a Gaza da kuma Lebanonin domin kawo karshen yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.