Kura na lafawa bayan rikici a Sri Lanka

Kura na lafawa bayan rikici a Sri Lanka
Shugaban kasar Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa ya bukaci al'ummar kasar da su guji duk wani yunkuri na tada zaune tsaye da ka iya haddasa rikicin kabilanci ko na addini.

Wannan kira ya biyo bayan rikici da ya barke a sassa daban-daban na kasar ta Sri Lanka kan rashin gamsuwa da kamu ludayin gwamnati na tafiyar da tattalin arzikin kasar. A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban Rajapaksa ya ce a wannan lokacin ne ya kamata 'yan kasar su hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da zamantakewa da kuma siyasa a kasar.

Mutane takwas ne suka rasa rayukansu a wannan makon yayin da 225 suka jikata a wata zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma a Sri Lanka, lamarin da ya Firministan kasar Mahinda Rajapaksa yin murabus. Tuni dai gwamnatin kasar ta bayar da umurnin harbe duk wanda aka kama da yunkurin lalata kadarorin gwamnati ko ma yin barazana ga rayukan jama'a. 
 


News Source:   DW (dw.com)