Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta dakatar da aiki a Sudan

Kungiyar Likitocin na gudanar da aiki ne na duba marasa lafiya a sansanin 'yan gudun hijra na Zamzam a lardin Al Fashir, inda mutane sama da rabin miliyan ke rayuwa a sansanin.

Karin bayani: Doctors Without Borders za ta bar Madagaska

Shugaban kungiyar likitocin ta Doctors Without Borders Yahya Kalilah, ya ce mataki na suka dauka mai tsarurin gaske da basu da zabi illa dakatar da aiki a Zamzam sakamakon tabarbarewar tsaro a Sudan.

Karin bayani: 'Yan gudun hijira da ke sansanin Jamam a Kudancin Sudan na cikin matsanancin hali

Ya kara da cewa tun daga farkon watan Fabrairun 2025, sun yi rajistar mutane akalla 139 da ke dauke da alburusai da kuma munanan raunuka a jikinsu, inda 11 daga cikinsu suka mutu ciki har da yara kananna guda biyar.

 


News Source:   DW (dw.com)