Kungiyar kasashen APEC na babban taro kan tattalin arziki

A wannan rana ta Juma'a wakilan kungiyar kawancen kasashen Asiya da Pacific 21 wato APEC ke fara babban taronsu na shekara shekara, wanda manyan shugabannin kasashen duniya ke halarta, da ke zama babban taronta na farko tun bayan sake zabar Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka.

Karin bayani:Indiya da Chaina za su yi sulhu kan iyakar da ke tsakaninsu

Daga cikin mahalarta taron na birnin Lima na kasar Peru har da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden da na China Xi Jinping, sai firaministan Canada Justin Trudeau da sabon shugaban Indonesia Prabowo Subianto, da firaministan Japan Shigeru Ishiba da takwaransa na Australia Anthony Albanese, da dai sauran shugabannin kasashen duniya.

Karin bayani:Putin ya karbi shugabanni a taron kolin BRICS

Kasashen APEC na zama wadanda ke samar da kashi biyu cikin uku na tattalin arzikin duniya, ta fannin kayayyakin da suke sarrafawa a kasashensu wato GDP.


News Source:   DW (dw.com)