Kungiyar kasashen G7 ta bayyana Rasha a matsayin wace ke kawo cikas ga duk wani yunkuri na warware rikincin Ukraine cikin adalci, a cikin wata sanarwa da ta fidda a ranar Asabar da ta yi daidai da cika kwanaki 1,000 da Moscow ta kaddamar da mamayar Ukraine.
Karin bayani: Na imanin cewa yakin Ukraine zai kawo karshe a lokacin mulkin Trump - Zelensky
Shugabannin manyan kasashen bakwai na G7 masu karfin tattalin arziki a duniya da suka hadar da Amurka da Faransa da Jamus da Japan da Kanada da Burtaniya da Italiya sun kuma kara jaddada ci gaba da bai wa Ukraine goyon baya har sai inda bukata ta tsaya.
Kazalika Kungiyar ta G7 ta yaba wa 'yan Ukraine kan jajircewa da juriyar da suka nuna don kare mutumci da martabar kasarsu duk da matsalolin na ruyuwa da Rasha ta jefa su a ciki.
Karin bayani: Rasha ta zargi Amurka da dakile sulhu a yakin Ukraine
Shugabanni na G7 sun kuma yi alkawarin zama tsintsiya madaurinki daya wajen ci gaba da labta wa Moscow takunkuman karya tattalin arziki tare domin karya logonta kan haramtacciyar mamayar da ta kaddamar wa Ukraine.