Kotun Namibia ta kori karar 'yan adawa da ke neman soke zabe

Kotun kolin Namibia ta kori karar da babbar jam'iyyar adawar kasar IPC ta shigar, tana neman ta soke zaben shugaban kasa na watan Nuwamban 2024 da jam'iyyar SWAPO ta lashe, wadda take rike da kasar tun a shekrar 1990 bayan samun 'yancin kai.

Karin bayani:Za a binciki sahihancin zaben Namibiya

IPC ta yi korafin cewa matakin da shugaban kasar Nangolo Mbumba ya dauka na yin karin kwanaki biyu don ci gaba da kada kuri'a a matsayin karan tsaye ga tanadin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya ce ya yi hakan ne bisa shawarar hukumar zaben kasar ECN.

Karin bayani:Mace 'yar takarar shugaban kasa a Namibiya

SWAPO ta samu kashi 57 cikin 100 na kuri'un, inda 'yar takararta Netumbo Nandi-Ndaitwah ta samu nasarar zama mace ta farko da ta lashe zaben shugaban kasar, yayin da 'dan takarar IPC Panduleni Itula ya samu kashi 25.5 cikin 100 na kuri'un zaben.


News Source:   DW (dw.com)