Kotun Manhattan da ke Amurka ta umarci shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump da ya gurfana gabanta a ranar 10 ga wannan wata na Janairu da muke ciki, don fuskantar hukunci kan zargin biyan toshiyar baki ga jarumar fina-finan batsa Stormy Daniels don boye alakar da suka yi tare, da yin karya kan hada-hadar kasuwancinsa da kuma cin amanar kasa.
Karin bayani:Tsohon shugaban Amirka Donald Trump zai gurfana a gaban kotu a Maris
Ko da yake alkalin kotun Juan Manuel Merchan ya bai wa Trump zabin halartar kotun ta bidiyo, a matsayin sassauci sakamakon hidindimun da ke gabansa na shirin sake karbar mulkin kasar.
Sannan ya yi izinar cewa ba lallai ne Mr Trump ya fuskanci wani hukunci mai tsauri a kan shari'ar ba.
Karin bayani:Kotu ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Donald Trump
A cikin wayan Mayun da ya gabata ne aka samu Trump da aikata laifuka 34 na cin amanar kasa, da bada bayanan karya kan cinkayyarsa da kasuwancinsa, har ma da biyan jarumar batsa Stormy Daniels dala dubu dari da talatin ta hannun lauyansa a shekarar 2016, a matsayin toshiyar baki kan mu'amalar da ta wakana a tsakaninsu.