Babbar kotun Amurka ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa sabon zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, bayan samunsa da laifin cin zarafin wata mawallafiya E Jean Carroll a shekarar 1996 tare da bata mata suna, inda kotun ta umarce shi ya biyata diyyar dala miliyan 5.
Karin bayani:Amrika: An samu Trump da laifukan tuhume-tuhume 34
Mr Trump ya jima yana musanta zargin cin zarafin E Jean Carroll, ko da yake ta gaza gamsar da kotun cewa ya yi mata fyade.
karin bayani:An fara shari'ar Donald Trump kan zargin bada toshiyar baki
A ranar 20 ga watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa ta 2025 za a sake rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka, don yin zangon mulkinsa na biyu.