Sai dai duk da cewa alkalin ya kyale zabbane shugaban na Amurka Donald Trump ba tare da yanke masa hukunci ba, hakan ba ya nufin ba a samu shugaban da ake shirin rantsarwa a karo na biyu nan da kwanaki 10 da aikata laifi ba. Da yake mayar da martani kan zaman kotun a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce da man can babu wani laifi da ya aikata. A watan Mayun bara ne kotu ta samu Trump da laifuka 34 na bayar da kimanin dalar Amurka dubu 130 a matsayin toshiyar baki ga wata jaruma a fina-finan batsa, domin samun damar lashe zabensa a shekara ta 2016. Trump dai na zaman mai laifi na farko a tarhin Amurka da za a rantsar a wani babban mukami, har na shugaban kasa da yake shirin dare wa kan madafun iko a ranar 20 ga wannan wata na Janairu da muke ciki.
News Source: DW (dw.com)