Kotu ta saki 'yan adawa 11 a Mali

A wannan Alhamis kotun kasar Mali ta ba da umurnin sakin 'yan adawa 11 da hukumomi suka kama bisa zargin neman kifar da gwamnati, bayan sun bukaci gwamnatin mulkin sojan kasar ta mayar da kasar bisa tsarin dimukaradiyya.

Karin Bayani: Assimi Goïta ya ba wa gwamnati umarnin shirya zabe a Mali

Mutanen 11 da kotu ta ce aka sake sun hada da tsaffin ministoci da shugabannin siyasa da suka saka hannu kan kudirin neman ganin an koma tsarin mulkin dimukaradiyya a kasar da ke yankin yammacin Afirka. Majiyoyin kotu sun tabbatar da sakin mutanen ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. Sojojin kasar ta Mali sun gaza cika alkawarin da suka dauka na mayar da kasar bisa tafarkin tsarin farar hula a watan Maris na wannan shekara ta 2024 kamar yadda suka yi alkawarin lokacin da suka kifar da gwamnatin kasar, sakamakon matsalolin na tsaro da kasar take fuskanta.

 


News Source:   DW (dw.com)