Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar lauyoyin tsohon shugaban suke yin kira da a cire babban mai gabatar da kara a shari'ar da ke tafiyar hawainiya.
Zuma da mulkinsa ya zo karshe a shekarar 2018 bayan kwashe tsawon shekaru 9, ya musanta zargin da ake masa na halasta kudin haram, ya na mai zargin babban mai gabatar da kara Billy Downer da na nuna bangaranci; sai dai kotun kolin kasar ta yi watsi da bukatar Zuma na sauya shi.
Kotun ta tsayar da watan Augustan wannan shekarar don ci gaba da zaman shari'ar Zuma, wanda hakan zai bai wa shugaban kotun kolin ya yi nazarin sake bai wa Downer damar ci gaba da shari'ar.