Kotu ta daure Suu Kyi kan cin hanci a Myanmar

Kotu ta daure Suu Kyi kan cin hanci a Myanmar
Zaman kotun da aka yi shi a asirce, ya sami tsohuwar shugabar da laifin karbar rashawa ta Euro 560,000 tare da karbar kyautar zinare daga wani tsohon ministan kasar. Sai dai tuni Suu Kyi din ta musanta tuhume-tuhumen.

Kotu a Myanmar ta yanke wa hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyidaurin shekaru biyar a gidan kaso bayan samun ta da laifin cin hanci. Hukuncin na wannan Laraba shi ne na farko a cikin zarge-zargen cin hanci da gwamnatin mulkin sojin kasar ke yi wa Suu Kyi.
 
A shekarar da ta gabata ce dai sojoji suka hambarar da Suu Kyi daga mulki.  Idan an hada da hukuncin wannan Laraba da tsohon hukuncin da wata kotun Myanmar ta yanke wa tsohuwar shugabar a baya, a yanzu Suu Kyi za ta yi shekaru 11 ke nan a gidan kaso.
 


News Source:   DW (dw.com)