Kotu ta dakatar da firaministan Thailand

Kotu ta dakatar da firaministan Thailand
Kotun tsarin mulki a Thailand ta dakatar da firaministan kasar Prayuth Chan-ocha daga aiki, a yayin da take nazarin bukatar korarsa. 'Yan adawa ne dai suka mika bukatar tsige shi, bayan da suka zarge shi da yin tazarce.

A hukuncinta na wannan Larabar, kotun ba ta bayyana lokacin da ta diba domin bayyana matsayarta kan laifin da ake zargin babban jami'in da aikatawa ba. To amma umurnin dakatarwar zai fara aiki ne daga yau (24.08.2022).

Kawo yanzu dai ba a bayyana sunan wanda zai rike mukamin firaministan ba. Sai dai a bisa dokokin kasar, daya daga cikin mataimakan firaminista ne ya cancanci rike mukamin, kafin kotu ta kammala shari'ar da ake yi wa Prayuth.

 


News Source:   DW (dw.com)