A makon da ya gabata ne shugaban majalisar, Alban Bagbin ya ce akwai kujeru hudu a majalisar da ba su da wakili. Babban alkalin kotun, ya ce idan aka yi la'akari da irin barnar da hakan zai yi ga mazabu da ke da dubun dubatar al'umma, ya zama wajibi kotu ta gaggauta magance wannan takaddama.
Karin bayani: Dambarwar siyasa a majalisar dokokin Ghana
Rikici ya kaure ne a tsakanin jam'iyyar shugaban kasar, Nana Akufo-Addo ta NPP da kuma jami'iyyar adawa ta NDC wadda ta samu karamin rinjaye bayan da wasu 'yan majalisu hudu suka sauya sheka. Kundun tsarin mulkin Ghana dai bai ba 'yan majalisa damar sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabe su ba.
Ana dai ganin kasar Ghana a matsayin kasar da ke da saukin rikicin siyasa a yankin Yammacin Afirka da ke fama da tarin rikice-rikice.