Koriya ta Kudu ta harba makami mai linzami cikin ruwan yammacin kasar, lokacin da sojojinta ke atisaye a wannan Juma'a, a wani mataki na gargadin makwabciyarta Koriya ta Arewa, wadda ita ma ta harba jerin makaman a kwanan nan.
Karin bayani:Koriya ta Arewa ta yi wa ta Kudu Kashedi
Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce gwajin makamin wata alama ce ta nunawa abokiyar gabarta Koriya ta Arewa cewa a tsaye take daram da kafarta bata tsoron ta kife, sakamakon yadda makwabciyar tata ke takalarta a kai a kai.
Karin bayani:Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami
A ranar Lahadin da ta gabata Koriya ta Kudu da Japan da kuma Amurka suka gudanar da rawar soji ta hadin gwiwa da nunin makamai, da suka hadar jiragen sama iri iri na yaki, don mayarwa Koriya ta Arewa martani kan gwaje gwajen da take gudanarwa a baya bayan nan, sakamakon zaman tankiya da ke kara zafi a yankin.