Koriya ta Kudu: Shugaba Yoon ya gurfana a gaban kotu

Shugaban kasar Koriya ta Kudu da aka tsige, Yoon Suk Yeol ya bayyana a gaban kotu a karon farko domin halartar zaman da zai yanke hukunci kan ko za a ci gaba da tsare shi, yayin da hukumomin kasar ke bincike kan yunkurinsa na sauya dokar sojin da bai yi nasara ba. 'Yan gani kashenin tsohon shugaban kasar sun yi dafifi a gaban kotun, kana wasu suka mamaye motar da ke dauke da madugun nasu.

Karin bayani: An gaza kama shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige

Gabanin fara sauraron shari'ar, lauyan da ke kare Mista Yoon ya ce, shugaban zai gurfana ne a gaban kotun domin ya dawo da martabarsa a idon jama'a.

Idan aka amince da bukatar masu binciken, za su iya ci gaba da tsare shi har na tsawon wasu kwanaki 20 wanda zai ba masu gabatar da kara isasshen lokaci kafin mika shi gaban kotu. Shugaba Yoon, wanda yi ikrarin cewa an kama shi ne ba bisa ka'ida ba, ya jefa Koriya ta Kudu cikin rikici ne a ranar 3 ga watan Disambar 2024, bayan da ya yi yunkurun kafa dokar soji wanda majalisar dokokin kasar ta dakile.

 


News Source:   DW (dw.com)