Koriya ta haramta amfani da manhajar DeepSeek

Hukumar da ke kula da tattara bayanan sirrin Koriya ta Kudu ce ta haramta amfani da manhajar, inda ta ce a halin yanzu babu wanda zai iya sauke manhajar a apple store. Kasashe da dama na dari-darin amfani da manhajar ta DeepSeek da ke da cibiya a kasar China.

Karin bayani: Taron koli kan fasahar kirkira ta AI

A farkon watan Fabrairun 2025, kasar  Australia ta haramtawa dukkan hukumomin gwamnati da na tsaro amfani da manhajar ta DeepSeek. Kazalika 'yan majalisar dokokin Amurka sun bukaci dakatar da amfani da manhajar a dukkan al'amuran da suka shafi gwamnati domin gudun fitar bayanan sirrin kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)