Guterres, wanda ya kai ziyarar kwanaki biyu a Koriya ta Kudu, ya bayyana cewa babban aikin da ke gabansa shi ne kawar da makaman nukiliyar Koriya ta Arewa don samar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin baki daya.
Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa, ta zargi MDD da yunkurin kare muradun Amirka. Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman da ba a taba gani ba a bana, wanda ya hada da harba makami mai linzami da ke tsakanin nahiyoyi a karon farko tun shekarar 2017.