Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya ce kara azama a kan kawancen hadin kai na tsaro a tsakanin kasashen Koriya ta Kudu da Japan da Amurka barazana ce ga kasarsa kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen daukar matakin kariya.
Da yake jawabi a taron cika shekaru 77 da kafuwar kasar a karshen makon da ya gabata, Kim ya ce kwanacen da Amurka ke jagoranta wani shiri ne da ke son matso da kungiyar kawancen tsaro ta NATO kusa, kuma ba zai lamunta ba.
Har wa yau, shugaban na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da karfafa shirinsa na samar da makamashin nukiliya.
Karin Bayani:Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabon makami mai linzami