Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami zuwa Tekun Japan a Litinin din nan, a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyara bankwana a makwabciyarta kuma abokiyar gabarta Koriya ta Kudu.
Shalkwatar tsaron Koriya ta Kudu ta ce ta hango makamin da ta bayyana a matsayin makami mai linzami mai cin dogon zango, kana kuma ta ce ta yi imani an harbo shi ne daga yankin Pyongyang da misalin karfe 12 na rana wato karfe uku na safe agogon GMT.
Har ila yau ita ma ma'aikatar tsaro ta Japan ta tabbatar da hango makamin da ke zama na farko da Koriya ta Arewa ke harbawa a cikin wannan sabuwar shekara ta 2025, sai dai ta ce da akwai alamun makamin ya sauka a cikin Teku.
Rikicin siyasa ya rincabe a Koriya ta Kudu
Wannan sabuwar barazana ta Koriya ta Arewa na zuwa ne a daidai lokaci da makwabciyarta Koriya ta Kudu ta fada cikin rikicin siyasa mafi muni a tarihinta, inda ake ta kai ruwa rana kan kama tsigaggan shugaban kasar Yoon Suk Yeol kan yunkurinsa na kafa dokar soji da bai yi nasara ba.