Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami a gabashin gabar ruwan kasar, wanda ke zama irin sa na farko a cikin sama da watanni biyu, domin zama gargadi ga abokan hamayya, a cewar ta.
Karin bayani:Koriya ta Arewa ta yi wa ta Kudu Kashedi
Makaman wadanda aka harba daga Pyongyang babban birnin kasar da safiyar Alhamis din nan, sun yi tafiyar kilomita 360 kafin fadawa cikin ruwa.
Karin bayani:Koriya ta Kudu na son yaukaka huldar kasuwanci da kasashen Afirka
Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar Japan ta fitar, ta yi tir da wannan gwaji, wanda ta bayyana a matsayin takalar fada da kuma ta da husuma a yankin, bayan da wasu daga cikin makaman suka fada kusa da kasarta.
A makon da ya gabata ne dai firaministan Japan Fumio Kishida ya kai ziyara Seoul babban birnin Koriya ta Kudu, da zummar nuna mata goyon baya a rikicinta da Koriya ta Arewa tare da kara karfafa alaka da ita.