Tuni dai mahukuntan Seoul suka nuna damuwarsu, inda majalisar tsaron kasar ta yi wani taro domin tattauna lamarin. A nasa bangaren ministan tsaron kasar Japan, Nobuo Kishi ya bayyana gwajin makamai masu linzamin na Koriya ta Arewa da neman tayar da zaune tsaye, wanda kuma ya ce ba za a lamunta ba. Koriya ta Arewa dai na fama da tarin takunkumai sanadiyyar shirinta na makaman nukiliya, sai dai a mahukuntan Pyongyang din na nuna halin ko in kula dangane da takunkuman.
Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Kudu Yonhap, ya ruwaito cewa Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami guda uku a kusa da Pyongyang babban birnin kasarta.