Kimanin mutane 11 ne suka rasa rayukansu a kasar Yuganda, cikinsu har da kananan yara biyu, sanadiyyar gobarar da wata tankar dakon mai ta yi a Kampala babban birnin kasar, kamar yadda rundunar 'yan sandan kasar ta sanar. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Patrick Onyango ya ce tankar man ta yi adungure ne bayan hatsarin da ta yi, sannan ta kama da wuta ta kone mutanen kurmus, ta yadda ba a iya gane kowa.
Karin bayani:Fashewar tankar mai ta haddasa mace-mace a Jigawa
Wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda mutane ke kwasar man bayan kifewar motar gabanin fashewarta, makamanciyar yadda ta wakana kenan a jihar Jigawan Najeriya a baya bayan nan, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 170.
Karin bayani:Tanka ta kashe rayuka a Tanzaniya
Ko a shekarar 2019 ma an samu irin wannan hatsari a kasar Tanzaniya da ya halaka mutane 62, sai wanda ya lakume rayukan mutane 183 a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2015.