
Italiya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara kafa wani kwamiti na masu shiga tsakani na kasa da kasa a kokarin cimma matsaya ta kai wa ga matakin tsagaita wuta a yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.
Shirin na Italiya ya zo ne a daidai lokacin da rikicin kasar ta Ukraine ke kara tabarbarewa, wanda ke yin barazanar kara ta'azzarar matsalolin makamashi da na abinci a duniya baki daya. Yayin da yake matukar kawo cikas ga ayyukan noma da fitar da cimmaka daga kasar Ukraine, zuwa kasashen waje. Kasar ta Ukraine dai ta kasance ta hudu a duniya wajen noman masara kana ta uku wajen noman alkama.
News Source: DW (dw.com)