Kokarin ceto bakin haure a ruwan Tunusiya

Kokarin ceto bakin haure a ruwan Tunusiya
Masu aikin ceto a Tunusiya na ci gaba da laluben mutane da dama da suka bace, bayan da nutsewar wani kwale-kwale makare da bakin haure.

Rahotanni sun nunar da cewa bakin hauren da suka fito daga Libiya, na kokarin tsallakawa Turai ne da suke yi wa kallon tudun mun tsira. Kwale-kwalen dai, ya nutse ne a gabar ruwan Tunusiyan. Hukumar Kula da Kaurar Jama'a ta Kasa da Kasa ta bayyana cewa an ceto mutane 30 yayin da wasu 75 suka yi batan dabo kana an gano gawar mutum guda, bayan da kwale-kwalen da suke cikin ya nutse a birnin Sfax da ke kudancin Tunisiya. Da yake karin haske kan batun maimagana da yawun mahukunta a birnin na Sfax Mourad Turki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na  Associated Press cewa, mutanen da aka ceto shekarunsu sun kama ne daga 18 zuwa 40 a duniya. Mutanen dai sun hada da 'yan kasashen Bangaladash da Masar da Maroko da kuma Kamaru.


News Source:   DW (dw.com)