Ko me yasa ba Messi a kyautar Ballon d'Or?

Ko me yasa ba Messi a kyautar Ballon d'Or?
A karon farko tun 2005, an cire sunan Lionel Messi cikin jerin sunayen 'yan wasa 30 da aka zaba don babbar kyautar Ballon d'Or, bayan da ya lashe kyautar har sau bakwai a shekarun baya.

'Yan wasan da aka zaba a 2022, sun hada da Lewandowski da Kylian Mbappe da Karim Benzema da Erling Haaland da Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kyautar sau biyar da Mohamed Salah da Sadio Mane da Kevin De Bruyne da Harry Kane da kuma Son Heung-min na cikin 'yan wasa 30 da za su kara a bana.

Messi mai shekaru 35, ya doke Robert Lewandowski a cin kyautar Ballon d'Or a 2021, amma bana baya cikin jerin 'yan wasan da aka zaba don cin kyautar sabdoa rashin nasara a kakar wasanni na farko a kungiyar Paris Saint-Germain.

Tun shekarar 1956 mujjalar Faransa kan harkokin wasanni ta fara ba da kyautar Ballon d'Or ga zakarun maza da ke murza leda, sai dai mujjalar gta fara ba da kyautar ga mata a shekarar 2018, kuma Ada Martine Rogne Hegerberg yar kasar Norwa ce ta fara samun kyautar.

A bana 'yan wasa mata 20 sun higa sahu, ciki har da Alexia Putellas da Ada Hegerberg da Sam Kerr da Vivianne Miedema. 'Yan wasan Amirka kamar Alex Morgan da Catarina Macario da Trinity Rodman suma suna cikin jerin Y'an wasa mata 20 da aka zaba don kyautar a bana.

Za a ba da kyautar a ranar 17 ga watan Oktoba 2022. Daga cikin sauye-sauyen da aka sanar a watan Maris kan kyautar, yanzu ana bayar da kyautar ne bisa la'akari da rawar da 'Yan wasa suka taka a kakar wasannin Turai, maimakon shekara ta kalanda.

Rage yawan masu kada kuri'a na cikin wasu sauye-sauye, da nufin daidaita tsarin. Har ila yau, masu jefa ƙuri'a ba za su yi la'akari da nasarorin da ɗan wasan ya samu ba.


News Source:   DW (dw.com)