Kindiki, wanda shi ne ministan harkokin cikin gidan Kenya, na daga cikin ‘yan takara da majalisar kasa ta tantancewa bayan da rikicin siyasa ya yi awon gaba da kujerar Rigathi Gachagua. Shugaba Ruto bai jira kwanaki 14 da dokokin Kenya suka amince da su wajen nada sabon mataimakin shugaban kasa ba, kuma tuni majalisar dokokin kasar ta kada kuri’a kan zabin nasa domin amincewa da shi, sabanin kwanaki 60 da aka tanada.
Karin bayani: Tsige mataimakin shugaban kasar Kenya
Kithure Kindiki mai shekau 52, tsohon malamin jami'a ne da ya zama hamshakin attajiri kafin ya zama minista, kuma ya yi nasarar kare shugaban Kenya yanzu William Ruto a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, bisa zargi marar hannu a laifukan da aka aikata a rikicin da ya biyo bayan zaben Kenya a shekara ta 2007. Sabon mataimakin shugaban kasar Kenya ya fito ne daga yankin tsaunuka na Kenya, amma yana shan suka dangane da goyon bayan 'yan sanda lokacin da zanga-zangar yaki da kara haraji wacce ta yi sanadin mutuwar matasa 60.