Kisan ungulu ya janyo shekaru 24 a kaso

Kisan ungulu ya janyo shekaru 24 a kaso
Wani alkalin gundumar Monterey ya ce kotu ta yankewa Ivan Gomez mai shekaru 31a duniya, hukuncin ne sakamakon kisan ungulu ta hanyar cinnawa gandun daji wuta, yayin da yake noma tabar wiwi ba bisa ka'ida ba.

Masu gabatar da kara a Amirka sun ce an yanke hukuncin shekaru 24 a gidan yari kan mutumin da ya fara haddasa gobarar dajin a shekarar 2020 a Carlifonia, wanda ya kashe ungulu 12 tare da jikkata wasu manyan tsuntsaye da jefa rayuwar jami'an kashe gobara a cikin hadarin gaske.

A ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 2020 ne gobarar ta tashi a gabar tekun tsakiyar Arewa maso Yammacin Los Angeles, inda ta lalata gidaje 10 da kadada 80 ta gandun dajin wanda tun a 1997 aka ware don 'yantar da ungulu.


News Source:   DW (dw.com)