Ma'aikatar muhallin ta ce baya ga mutumin da ya rasa ransa kifin ya kuma jikkata wani 'dan yawon bude ido gudu da ke karbar magani a asibiti.
Karin bayani: Nijar ta dage dokar hana noman tattasai da kamun kifi a Diffa
Hukumomin Masar basu sanar da sunaye da kuma kasashen da mutanen da suka gamu da fushin mari babban kifin a tsibirin Marsa Alam suka fito ba.
Karin bayani:
Wuraren yawon bude ido a Afirka
Afirka na da kasashe sama da 50. Wakilin DW Adrian Kriesch ya kwashe fiye da shekaru goma a nahiyar kuma ya lissafo wasu daga cikin wuraren da ke daukar hankalin 'yan yawon bude ido a nahiyar.
Hoto: Adrian Kriesch/DWTsibirin Comoros
Ina sha'awar zuwa Comoros, tsibiri mai aman wuta da ke tekun Indiya a tsakanin kasashen Mozambik da Madagaska. Ya kasance teku mafi tsaftataccen ruwa da na taba gani a Afirka. Tsibirin gwanin sha'awa amma ba duk masu yawon bude ido suka san da shi ba. Yanayin zafi a nahiyar, ya sa yana yawan cika da masu son shakatawa.
Hoto: Adrian Kriesch/DWMauritius β Kasar da ke a tsakanin nahiyoyi biyu
Masu son jin dadin rayuwa su ziyarci Mauritius. Tsibirin da ke tekun Indiya na da manyan otel-otel a daf da rairayin bakin tekun mai fadin gaske. Baya ga kasancewar kasar a tsakanin nahiyar Afirka da Asiya ta la'akari da al'adu, akwai dazuzzuka da tsaunuka a yankin, gwanin sha'awa.
Hoto: Roberto Moiola/robertharding/picture allianceTsibirin Zanzibar βAl'adu
Duk da cewa ya shahara ga masu yawon bude ido, tsibirin Zanzibar na Tanzaniya, ya kasance daya daga cikin wuraren da na fi so. Baya ga kyawawan tekuna, wajibi ka ziyarci wurin da ake kira ''Stone Town'' birni mafi dadewa a Zanzibar. Nan za ka kashe kwarkwatar idanunka a kallon kayayyakin al'adu masu dimbin tarihi. Kowane maraice ana girka abincin sayarwa kala-kala a kasuwar abinci ta Forodhani.
Hoto: Stefan Auth/imageBROKER/picture allianceTsibirin Sao Tome da Principe
Tsibiri na karshe a kundina, a wannan karon na yada zango a Guinea da ke a yankin yammacin Afirka, tsibirin Sao Tome da Principe, mai al'uma sama da dubu dari biyu. Abin mamakin shi ne, masu yawon bude ido da dama ba su san da wannan tsibirin ba, bugu da kari, jiragen sama kalilan ne ke iya zuwa tsibirin.
Hoto: Sebastian Kahnert/dpa/picture allianceBirnin Cape Town
Wuri ne mai saukin zuwa don masu yawon bude ido ka iya samun jirgin da zai kai su har birnin na Cape Town. Birnin mai katafaren tashar jiragen ruwa na a yankin kudu maso yammacin Afirka ta Kudu zagaye da tsaunuka masu ban sha'awa. Duk da cewa ba boyayyen wuri ba ne, na zauna a nan ina kuma matukar kaunar birnin. Ga masu son sha'awar ninkaya, wannan wata dama ce, ga kuma damar zagaya gonar inibi.
Hoto: Adrian Kriesch/DWDalar Nubian na Sudan
Al'umar Sudan na da karamci. Wani abokina dan Sudan cikin raha ya ce, zumuncinmu da tsauri, don kusan koyaushe sai an gayyaci bako shan shayi. Kalilan ke iya kai ziyara kasar, musanman ganin yadda gwamnati ke gargadin baki kan su yi taka tsan-tsan, saboda rikicin masu gwagwarmaya da makamai a wasu sassan kasar. Idan ka sami kanka a Sudan, kada ka tafi ba tare da ka kai ziyara dalar Nubian ba.
Hoto: Adrian Kriesch/DWNi'ima a Namibiya
Kasar ba ta da yawan jama'a, tana yankin Kudu maso yammacin Afirka, kasa ce mai alfahari da hamada. Akwai dai kalubale na zirga-zirga, dole ka shirya yin dogon tuki ga masu ziyara. Namibiya na da wuraren shakatawa da gandun dazuka da ake ajiye da namun daji iri daban-dabam.
Hoto: Adrian Kriesch/DWWurin nishadi a birnin Legas
Idan burinka nishadi ba tare da ka damu da hayaniya da kacaniya ba, to ka ziyarci birnin Legas da ke Najeriya, mutum sama da miliyan ashirin ke zaune a birnin. Cunkus dakin tsumma amma a fannin al'adu, birnin gwanin sha'awa, daga kayayyakin ado da raye-raye, ku garzaya Afrika Shrine, gidan shahararren mawaki marigayi Fela Anikulapo Kuti da yanzu magajinsa Femi Kuti ke nishadantar da baki.
Hoto: Adrian Kriesch/DWKyawawan gine-gine a Maputo
Maputo,babban birnin kasar Mozambik na yankin Kudu maso gabashin Afirka. Birnin na alfahari da tsofaffin gine-gine tun na zamanin Turawan mulkin mallaka na Portugal, kuma har yanzu suna nan gwanin ban sha'awa. Baya ga haka akwai wuraren shakatawa da ke bakin tekuna a gabar ruwa da ke sassan kasar.
Hoto: Adrian Kriesch/DWHotuna 91 | 9Hotuna 9Ma'ikatar ta ce lamarin ya faru ne a wani waje da tsibirin wanda kuma aka haramta kai koma a yankin. Makamancin wannan al'amari ya kuma faru a shekara ta 2023, da wani gawurtaccen kifi ya halaka wani 'dan kasar Rasha shiyyar Hurghada da ke Marsa Alam.
Ko a watan Nuwambar 2024, wani jirgin 'yan yawon shakatawa ya kifi a wannan waje da yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare kuma da wasu mutanen bakwai da suka bace.