An kashe mutane hudu tare da raunata biyar a kudancin Kenya a lokacin da aka sha arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna adawa da karuwar hare-haren da namun daji.
'Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zangar a garin Masimba mai tazarar kilomita 170 a kudu maso gabashin Nairobi babban birnin kasar. Wadanda suka fusata da mutuwar wani malamin makarantar da giwa ta kashe.Sun kona tayoyi tare da rufe hanyar da ta hada Nairobi da Mombasa mai tashar jiragen ruwa.
News Source: DW (dw.com)