Kentucky: Ambaliya ta yi mummunar barna

Kentucky: Ambaliya ta yi mummunar barna
Akalla mutane guda 16 ne suka mutu a ambaliya mafi muni a tarihin Jihar Kentucky ta Amirka.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afka wa gabashin jihar a daren Laraba zuwa Alhamis,inda ya mayar da wasu tituna tamkar koguna tare da tilastawa mazauna wurin samun mafaka a rufin gidajensu, yayin da suke jiran taimako. An yi gargadin cewar adadin wadanda suka mutun zai iya ninka har sau biyu,saboda yadda har kawo yanzu ake ci gaba da shatata ruwan sama marka-marka a jihar: Shugaba Joe Biden ya ayyana dokar yanayi na halin iftala'i tare da fitar da tallafin tarayya don tallafa wa yankunan da guguwa, da ambaliya, da zabtarewar kasa suka shafa.

 


News Source:   DW (dw.com)