Kazakhstan ta gyara kundin tsarin mulki

Kazakhstan ta gyara kundin tsarin mulki
Al'uma a kasar Kazakhstan sun nuna goyan bayansu ga shirin Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

Al'umar kasar Kazakhstan sun nuna goyan bayansu ga shirin Shugaba Kassym-Jomart Tokayev  na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska kamar yadda sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar a kasar a ranar Lahadin da ta gabata ya nunar. Kashi saba'in da bakwai cikin dari sun goyi bayan shirin shugaban.

An yi zaben neman amincewar 'yan kasar, bayan da shugaban na Kazakhstan, ya sha alwashin inganta tattalin arziki da rayuwar 'yan kasa a wasu sabbin tsare-tsare da ya shirya aiwatarwa nan bada jimawa ba.

Amma masana sun alakanta shirin nasa da siyasa, da ake ganin wani sabon yunkuri ne na neman wa'adin shugabancin kasar a karo na biyu. Kasar mai arzikin man fetur ta soma farfadowa daga wani kazamin rikici da ya kusan durkusar da kasar a sakamakon yunkurin da wasu suka yi na kifar da gwamnati a watan Janairun da ya gabata.


News Source:   DW (dw.com)